Bakori zai jagoranci kwamitin yaɗa labaran Tinubu/Dikko 2027
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙwararren ɗan jarida, Ahmad Abdulkadir Bakori, zai jagoranci kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da kafafen yaɗa labarai na kamfen ɗin Tinubu/Dikko 2027, yayin da kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Katsina, Dr. Bala Salisu Zango, zai zama sakataren kwamitin.
Kwamitin zai kula da yaɗa saƙonnin kamfen, hulɗa da kafafen yaɗa labarai da kuma daidaita sadarwar kamfen da jama’a.
Naɗin ya kasance wani ɓangare na tsarin gudanar da harkokin yaɗa labarai da sadarwa na kamfen ɗin Tinubu/Dikko na zaɓen 2027.
Ahmad Abdulkadir tsohon shugaban gida talabishin na Jihar Katsina yayi aiki a hukumar NBC inda yakai matsayin darakta.
The full article is being collected. Available text is shown for now.